31 Janairu 2022 - 19:21
​Ra’isi: Iran Za Ta Fara Aiwatar Da Wasu Sabbin Tsare-Tsare Na Tattalin Arziki

Shugaban kasar Iran Ibrahim ra’isi ya bayyana cewa, kasar za ta fara aiwatar da wasu sabbin tsare-tsare na bunkasa harkokin tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Irahim Ra’isi ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake bayani kan shawarwarin da jagoran juyi na kasar ta Iran ya bayar kan daukar matakai na kara bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar, ta hanyar jajircewa da kuma dogaro da kai.

Ra’isi ya ci gaba da cewa, sabbin tsare-tsaren za su mayar da hankali ne wajen bunkasa ayyukan sana’oin cikin gida da kamfanonin kasar suke yi, da kuma yin amfani da wasu hanyoyi na daban-daban da ba su da alaka da samun kudi daga hanyar man fetur ko iskar gas da kasar take sayarwa.

Haka nan kuma shugaban an Iran ya jaddada cewa, dukkanin shirin nasu ba zai dogara da dage takunkumin Amurka akan Iran, ta yadda za a ya aiwatar da shi ko da takunkumi a kan Iran ko babu takunkumi.

Yanzu haka dai Ibrahim Ra’isi ya umarci mataimakinsa Muhammad Mukhbir da ya kafa kwamitin da zai fara aikin, wanda zai kunshi masana a bangarori daban-daban na harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kasar.

Ra’isi ya ce aiwatar da wannan tsari zai baiwa kasar Iran damar cimma burinta na habaka tattalin arzikinta, da kuma ci gaban gaban masana’ntu na cikin gida.

342/